Gwamnan Kano ya turawa majalisar dokoki sunan wanda zai naɗa a matsayin kwamishina

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamna Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tura sunan wani tsohon soja ga majalisar dokokin Jihar kano domin tantace shi a matsayin kwamishina.

Wanda a ka tura ɗin shi ne Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya.

Shugaban majalisar Isma’il Falgore ne ya karanta wasiƙar da gwamnan ya tura musu, yayin zaman majalisar na wannan rana ta Talata.

Majalisar ta buƙaci wanda aka tura sunan na shi da ya gurfana gaban majalisar gobe Laraba domin tantancewa.

By ukarofi