Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Ƙungiyar Sawaba reshen Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na Jihar ta Jigawa kwamared Bashir Kashim Bash ta nuna damuwar ta kan yanayin rayuwa da ‘yan Nijeriya suke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar kayan masarufi da matsalar rashin tsaro a wasu sassa na arewacin Nijeriya .
Shugaban yaci gaba da cewa, faɗuwar darajar Naira a kasuwar duniya da ciyo bashin bankin duniya da IMF wanda gwamnatin tarayya ta keyi babu ƙaƙƙautawa yana daga cikin abubuwan da suka ƙara durƙusar da Nijeriya su ka tsunduma ‘yan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa
Haka zalika ya soki lamirin gwamnatin da ta fito da wasu tsare tsare wadanda za su sanya al,ummar ƙasa cikin mawuyacin halin rayuwa ,misali rufe Kan iyakokin ƙasar nan tare da janye tallafin man fetur da gwamnatin tayi shine ya Kara dagula al,amuran rayuwar al,ummar wannan ƙasa tamu Nijeriya .
Ƙungiyar ta Sawaba tayi tir da wasu da dama daga cikin tsare tsaren shugaban ita wannan ƙasa wadda ta sanadinsu ne a ka ƙara jefa rayuwar talakawan wannan ƙasa cikin wani halin wahala da ƙuntatawa .
Ya ƙara da cewar Ƙungiyar Sawaba za ta ci gaba da abinda takeyi na sadaukar da rayuwarta wajen ganin talakawan Nijeriya sun sami sa’ida har sai abubuwa sun koma daidai domin kyautata rayuwar mutanen Nijeriya
Bash ya ƙara da cewa, su fa ba su da burin da ya wuce su ga talakawan Nijeriya da matasan su musamman na Jihar Jigawa suna cikin walwala da annashuwa, ma’ana wato Sawaba .
Ya ƙara da cewar kungiyar su ta Sawaba tana samun kiraye kiraye daga ‘yan Nijeriya waɗanda su ke cikin ƙuncin rayuwa musamman a kan zanga-zangar da ‘yan Nijeriya suke Shirin faɗawa a ranar ɗaya ga watan Agusta Kamar yadda dokar ƙasa ta ba su dama Kuma ta sahale masu yin ta .
Kashim ya nuna damuwarsa matuka gaya akan yadda ‘yaƴan ƙungiyar su ke fuskantar matsin lamba daga jami’an tsaro da gwamnati a lokacin da su ka amsa gayyata kala kala daga ofishin Jami’an tsaro har ma da ita kanta gwamnatin Jihar Jigawa a kan wannan al’amari daya shafi ‘yan Nijeriya Kai tsaye
Hakan yasa a ka tilasta ƙungiyar ta Sawaba ta bi sahun ‘yan uwan ta wato sauran ƙungiyoyin da ke Nijeriya ta bayyana matsayinta a mungiyance na cewar Sawaba ba za ta fito tayi zanga-zangar ba, amma Kuma ba za ta hana duk wanda ya ke da ra’ayin yin zanga-zangar ba yayi domin nuna damuwarsa ga gwamnati kamar sauran ‘yan Nijeriya ,amma duk wanda ya shiga zanga-zangar,ya shige ta ne bada yawun ƙungiyar ta Sawaba ba .
Ya ƙara da cewar ƙungiyar Sawaba ba ta da ikon hana ‘yan ƙasa fitowa suyi zanga- zangar, amma ita ƙungiyar Sawaba ta janye daga yin zanga-zangar da ‘yan ƙasar su ke shirin aiwatarwa, sai dai kuma ba su da hurumin hana dukkan ‘yan ƙasar fitowa su nuna damuwarsu kamar yadda dokar ƙasa ta basu dama domin jama’a ba a ƙarƙashin ikon Sawaba su ke ba .
Malam Kashim ya ƙara da cewar Ƙungiyar su ta Sawaba ba ta jingina da wata ƙungiya ba walau daga ciki ko wajen Nijeriya a kan abinda ya shafi wannan zanga-zanga, lamari ne na ‘yan kasa wanda ita Sawaba ba ta da ikon hana su saboda matsalar su ce da ta shafesu kai tsaye.
Daga nan ya bayyanawa ya’yan ƙungiyar ta Sawaba cewar dokar ƙasa ta ba su damar yin zanga-zanga kamar yadda ya ke a cikin dokar ƙasa, kowa na iya shiga sahun ‘yan Nijeriya a yi zanga-zanga da shi ko Kuma ya zauna a gida ya yi ta yin addu’ar zaman lafiya. Amma duk wanda zai fita zanga-zangar ya sani ya fita ne dan ƙashin kansa ba da sunan kungiyar Sawaba ba inji shugaban kungiyar
