Kiristoci sun ba Musulmai kariya wajen zanga-zanga yayin da suke sallar Azahar

Spread the love

A wani abun farin ciki da ya faru yayin zanga-zanga a Jos, shine kiristoci sun ba Musulmai kariya yayin da suke sallar Azahar a filin zanga-zanga.

Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin addini yayi ƙamari a jihar amma da irin wannan haɗin kan, za a iya cewa lallai matasa sun fara gane abunda ke masu ciwo kuma za su kawo cigaba nan gaba mai ɗorewa.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, wannan abun da ya faru ya nuna cewa, kiristoci da Musulmai kan su haɗe yake, wasu ɓatagari ne ko a can baya ke son raba wannan haɗin kan.

Kuma wannan wata alama ce da ke nuni da cewa, in dai muka haɗa kawunanmu to za mu samu cigaba fiye da yadda muke tunani. Kuma wannan hotunan da ke yawo zasu ƙara na saura sassan ƙasar nan ƙwarin gwiwa yadda ya dace.

By ukarofi