
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Jami’an tsaro sun tarwatsa ƴan zanga-zanga bayan da su ka riƙa ƙona tayoyi da wasu abubuwa a wajen Fadar gwamnatin Jihar Kano.
Ƴan zanga-zangar sun taru ne daga sassa daban-daban na Jihar a inda su ke jira gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar mu su da jawabi.
Yayin haka ne su ka mayar da taron ya koma hayaniya inda ƴan sanda da sauran jami’an hukumomi su ka ɗauki matakan da su ka dace game da al’amarin.
