Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana fita zuwa awanni 24.
Gwamna Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a yanzu lokacin da ya ke ma manema labarai ƙarin bayani.
Gwamna ya bayanna cewa ɗaukar wannan doka na da nasaba da yunƙurin da ake yi na cigaba da tashe-tashen hankula dake gudana da sunan zanga-zangar lumana da ake gudanarwa a faɗin Ƙasar nan baki ɗaya.
Gwamnan ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙwazo wajen aiwatar da aikin su dan kare al’umma da dukiyoyin su.
