Zanga-zanga: APC a Zamfara ta zargi PDP da ɗaukar nauyin kai hari gidan Matawalle

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta zargi jam’iyyar PDP da ɗaukar nauyin ‘yan bangar siyasa da suka kai hari gidan tsohon gwamna kuma ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Muhammed Matawalle da ke Gusau yayin zanga-zangar da aka gudanar a faɗin kasar nan a yau.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris.

“Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta damu da yadda zanga-zangar lumana taso ta sauya sabon salon kai farmaki ga wasu jigajigan ‘ya’yan ta a jihar”.

“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda a ranar farko ta Zanga-zangar, a yau Alhamis, ‘yan barandan PDP da suka nufi gidan tsohon Gwamna Bello Mohammed Matawalle domin aiwatar da ɓarna amma jami’an tsaro suka yi gaggawar shiga tsakani suka tare su”.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa, ‘yan bangar siyasar ta PDP sun so su ƙona gidan minista Matawalle a yayi harin.

“Tabbas, jam’iyyar APC, musamman shugaban mu kuma ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle ba zai bari a sake irin wannan hali na dabbanci ba”.

A cewar Jam’iyyar ‘yan barandan na Jam’iyyar PDP sun kai hari gidan Sanata Sahabi Ya’u da ke mahaifar sa a garin Kaura Namoda inda suka lalata masa kaya da dama tare da lalata motarsa ​​kirar Toyota hilux da sunan zanga-zangar lumana.

“Tun da farko mun yi hasashen yiwuwar tada hargitsi a lokacin zanga-zangar a Jihar Zamfara, sai gashi hakan ta faru”.

Jam’iyyar ta APC ta roƙi jami’an tsaro a jihar da su baiwa mambobin ta da duk al’ummar jihar kariya da ake buƙata ga rayuka da dukiyoyin su baki ɗaya.

Hakazalika ta yi kira ga matasa da kada su bari miyagun ‘yan siyasa su yi amfani da su, musamman ganin yadda zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar ya ta kasance a wasu sassa cikin lumana na neman gwamnatin ta magance matsalolin wahalolin rayuwa.

“Wannan zanga-zangar, wacce haƙƙin ‘yan Nijeriya ne, ya kamata ta kasance cikin lumana ba tare da wata barazana ga rayuwa da dukiyoyin al’umma ba”.
Jam’iyyar ta yaba da jajircewar jami’an tsaro a jihar tare da kira garesu dasu Ƙara ƙaimi wajen kare rayuwa da dukiyoyin al’umma .

By ukarofi