Lamunin karatun gaba da sakandire ya je hannun ɗaliban Jami’o’i 6 a Nijeriya

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A yanzu jami’o’in gwamnatin tarayya guda shida da ɗalibansu ne suka ci gajiyar kashin farko na lamuni daga asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya NELFUND. Jami’o’in sun haɗa da; Jami’ar Benin dake Jihar Edo; Jami’ar Ibadan dake Jihar Oyo, Jami’ar Bayero dake Jihar Kano da Jami’ar Ilorin dake Jihar Kwara.

Ragowar sun haɗa da Jami’ar Maiduguri ta Jihar Borno da Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma a Jihar Katsina.

A halin yanzu an bada tallafin na kuɗi da ya kai Naira Biliyan Biyu da Miliyan Ashirin da shida da dubu ɗari da sittin da uku da ɗari uku da arba’in (N2,026,163,340). Wannan na daga yunƙurin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa dukkan ɗalibai basu samu tsaiko a karatun su ba saboda matsalar kuɗi.

By ukarofi