Boko Haram da ISWAP sun kashe mutane 109 cikin wata shida – Rahoto

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wani sabon rahoto da ‘Nextier’ ta fitar, ya ce aƙalla mutane 109 ne ayyukan ta’addanci ya yi sanadiyyar mutuwarsu a hare-hare 19 da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP su ka kai a wurare mabanbanta a rabin farko na shekarar 2024.

Rahoton ya ce, cibiyar kula da lamurran ta’addanci da ƙalubalen sansanin ƴan gudun hijira na Arewa-maso-Gabas ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta haɗe kai da maƙoftan ƙasashe domin inganta tsaro a kan iyakokin ƙasashen.

Dakta Chukwuma Okoli na jami’ar Azikwa da ke Akwa a Nijeriya ya wallafa rahoton tare da haɗin-gwiwar Dakta Ndu Nwokolo inda su ka fitar da yalwataccen bayani game da ta’addanci a shiyyar.

Rahoton ya ce jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da; Borno, Adamawa da Yobe waɗanda ƙananan hukumominsu su ka yi iyaka da ƙasashen Chadi, Nijar da Kamaru.

Daktan ya ce, la’akari da tsukun da wasu yankuna da ke ƙananan hukumomin ke da su da ake fama da ta’addancin, wuraren su na da wuyar kutsawa ga al’umma da ma hukumomin tsaro.

A sakamakon haka ne, mayaƙan su ke samun damar kai hare-hare daga waɗannan ƙauyukan wa sojoji da al’ummar gari.

Haka nan a cikin rahoton, Okoli ya shawarci gwamnatin Nijeriya tare da takwarorinta da su yi aiki tare da masu-ruwa-da-tsaki wajen ganin an samar da hanyoyin da za su taimakawa kawo ƙarshen tasirin ƴan ta’addan ga yankin da ma Ƙasa baki ɗaya.

By Babaji