Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shahararren mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya ce sukar da ake yi masa ba zai tilasta masa janye goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu ba.
Rarara ya bayyana cewa ba zai juya wa shugaban ƙasar baya ba ne a yayin wata hira da aka yi da shi a kafar DLC Hausa.
A kwanakin baya Facebook ya rufe shafin mawakin bayan masu goyon bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Nijeriya sun kai ƙarar shafin nasa.
Sai dai a yayin tattaunawar, Rarara ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya samo asali ne daga irin ƙoƙarin da shugaban ƙasar wajen tunkarar matsalolin da ke ci wa Nijeriya tuwo a ƙwarya.
A cewar mawakin, samar da Ma’aikatar Kiwo da Hukumar Raya Arewa maso Yamma da kuma ba wa ƙananan hukumomi ’yancin gashin kansu, an yi su ne domin yaƙar yunwa da fatara da rashin tsaro a Arewa.
Mawaƙin ya ƙara da cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa ayyukan Shugaba Tinubu za su samar da sakamako mai kyau a cikin watanni uku masu zuwa.
A cewar Rarara, Shugaba Tinubu ya cimma muhimman nasarori da shugabannin da suka shuɗe ba za su iya ba.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya musamman na Arewa da su shiga gangamin haɗin kai don jinjina wa gudunmawar Tinubu ba Nijeriya.
Haka kuma ya shawarci shugabannin ƙananan hukumomi da su sarrafa kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya yadda ya kamata.
