Gwamnoni ne matsalar Nijeriya – Kwamared Usman Okoi

Spread the love

Ɗan gwagwarmayar nan haifaffen Jihar Kogi, Usman Okai Austin wanda yayi takarar majalisar tarayya ya bayyana cewa gwamnoni ne matsalar ƙasar nan Nijeriya.

A wani martani ya mayar a kan jawabin shugaban ƙasa, ya bayyana cewa mafi yawan matsalolin nan daga gwamnoni suke, sun yi nasarar daƙile ƙananan hukumomi sannan ba su ba kotu daraja da masarautun gargajiya.

Okai ya caccaki ƙungiyar gwamnoni a matsayin maƙiyan al’umma domin sun fifita maslahar su a kan ta mutanen da suke mulka.

Abun kunya ka ji gwamnoni na sukar shugaban ƙasan alhalin suma ba mutanen kirki bane inji shi.

By ukarofi