
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ofishin jakadancin Rasha a Nijeriya ya musanta ya na da hannu a cikin ɗaga tutar ƙasarsa da wasu masu zanga-zanga ke yi a Arewacin Nijeriya.
An ga masu zanga-zangar su na tattaki a cikin gari ɗauke da tutocin su na rera waƙoƙi wasu kuma sun ɗaga takardu da ke ɗauke da wasu saƙonni.
Ƙasar Rasha ta kasance mai ikon faɗa-a-ji a duniya wanda hakan ya sa ake zargin ta na da hannu a sauyin siyasar wasu ƙasashen yammacin Afirka kamar su Nijar, Mali da Burkina Faso.
Sai dai a wani sanarwa da ofisoshin ya fitar a ranar Litinin, ya ce Rasha ba ta shiga al’amuran cikin gida na wasu ƙasashen, ya na mai cewa hakan da matasan su ka yi bai sanya Rasha ɗaukar wata matsaya ba.
Shugaban Ma’aikatan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya ce yin hakan cin amanar ƙasa ne inda ya ce za su ɗauki matakin doka akan su.
Janar Christopher ya ce, ga waɗanda ke kira a yi juyin mulki a Nijeriya, su sani hakan abu ne da ba za a bari ya faru ba domin rundunar soji ta amince da tsarin demokraɗiyya.
