MAKAMASHI: Biri ya yi kama da mutum

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Kace-nace da ake yi tsakanin hamshaƙin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko ɗangote, mai matatar man fetur, wacce babu kamarta a wannan nahiya ta Afrika da mashahurin ɗan kasuwa ɗan takarda, kuma daddigar ƙaya a wannan yanki na Arewa, wanda shine shugaban hukumar kula da haƙowa da sarrafa ɗanyen mai ta Najeriya (NMDPRA), Alhaji Injiniya Farouƙ Ahmed, daga zantukan nasu yana nuni da cewa, maganganun ɗangote yana fassara karin maganar nan da ke cewa, “biri ya yi kama da mutum”.

Duk da cewa, wannan fili ba Kotun ƙoli ta tarayya ba ne, kuma ba babban lauya ba ne mai matakin SAN kuma mai kare matatar ɗangote be, a matsayin wannan fili na ɗan kallo, amma duk da haka zan yanke hukunci na ce, ɗangote ya fi injiniya Farouk gaskiya daga yadda ya amsa tambayoyin Blueprint Manhaja da kuma kalaman da ya fito daga Majalisar Wakilai, wacce ta yi Kkira a gaggauta dakatar da shi wannan shugaba na wannan hukuma ta NMDPRA, Injiniya Farouk.

Hukumar NMDPRA da ta NNPCL da farko sun ɗauka cewa, burin ɗangote na samar da matatar man fetur da ta ke kan takardu, wato “Business Proposal; magana ce ta mafarkin rana irin na ɗan kasuwa, sun manta Aliko ba kanwar lasa ba ne, ɗan gado ne a harkar neman kuɗi daga tushe, kakansa na wajen mahaifinsa ɗan kasuwa ne mai nasibi a harkar ciniki, haka kakansa na wajen uwa hamshaƙin ɗan kasuwa ne, sai da ya yi zarra a harkar kasuwanci a duk sashen Afrika ta Yamma.

Tarihi ba zai manta da Alhaji Alhassan ɗantata ba a harkar kasuwanci. A lokacin da ya fito da dukiyarsa za a kai banki sai da takarkaru 30 aka yi mu su kayan taiki, kowanne ɗauke da sama da Naira miliyan na farin kuɗi, wato wuri aka yi ma sa musaya da Aninai da ɗarirrika da kwabbai da sisina da tararai da kuma sululluka dukkansu jan kuɗi.

A lokacin bayinsa sama da dubu sun bazama da kuɗaɗe fiye da Sulai 10, domin sayen amfanin gona, auduga da gyaɗa da riɗi da fatu da kuma ƙiraga, domin siyarwa ga Turawan Ingilishi da Faransa da kuma na Jamus da na Potugal.

’Yan takardar Arewa na yanzu sama da kashi 80 ’ya‘yan talakawa ne da suka mori dukiyar ƙasar nan ta wacikatashi da kuma babakere.

Hana ɗangote lasisi ba zai hana shi kasuwancinsaba, amma kada ku tunzura mana shi ya fasa kasuwancin ma’adanai irin na ƙarafa. Ku ƙyale mana shi hankalinsa ya je ga Ajakuta ko Katsina Rawlings ko kuma ma’aikatar mulmula ƙarafa ta Sokoto. Kai, ko wajen haƙar da gorar ruwa ruwai a Jihar Kano mutane sama da 10,000 ne za su samu ayyukan yi.

Rashin kishin ƙasa ya hana matatun man fetur na Kaduna da Warri da kuma na Fatakwal ƙin aiki. Haka kuma rashin kishin kai ya kawo haɗin baki da Turawan Yamma da na Amurka, shi ya kawo dukkan matsalolin da ake fuskanta a makamshi (energy), fannin ma’adanai (minerals) da kuma ƙarfin wutar lantarki (Power). Marasa kishin kai ne suke maƙarƙashiya (sabotage) suka sa Nijeriya ta ke tangal-tangal, mai ceto ta ya fito, amma suke tunzura shi ya ce ya fasa.

“Hassada ga mai rabo taki ne”, kuma sun manta, da cewa, ɗan zaki ya girma, haka kuma har ya karɓi sarautar sarkin mayu, don kuwa ya ci dubu sai ceto. Mutumin da ya doshi shekaru 70, yaya mafarauta tare da kanni kansu za su yi da shi? Amsa ita ce, sun yi sake, illa kawai su bayar da dama wannan aiki ya tabbata.

Idan man nan ya samu, ’yan Nijeriya sama da miliyan 200 za su amfana. Kiranmu ga Hukumar NMDPRA da Kamfanin NNPCL shine su natsu kuma hankalinsu ya dawo jikinsu su yi abin arziki, su yi abin da yakamata.

Ciwon hassada shine ciwon da ya ke kan gaba daga dukkan ciwokan da suke da alaƙa da zuciya da ruhi, kamar allura da zare ne ba ta ɓata. A fake da cewa, ba a kammala aiki ba shi ya sa ba a ba shi wannan lasisi ba, wannan zuƙi ta malle ce. Ku ba shi kaya, mu kuma masu saye mu ne da iko da za mu tabbatar da kayan na da iko da za mu tabbatar da kayan na da inganci ko kuwa.

Saboda haka mun goyi baya da a dakatar da Injiniya Farouk Ahmed daga daga kan kujerarsa har sai an gama bincike, kamar yadda kwamatin da majalisa ya bayar da shawara da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.

Zaman Injiniya Farouk da muƙarrabansa a kan wannan kujera haɗari ne ga tabbatuwar wannan matata ta ɗangote.

A ba wa kowa ne idan har zai biya wa matatar man fetur ta ɗangote burinta ba, mu mu na goyan dakatar da Injiniya Farouk. 

Idan matatu na Nijeriya suka gyaru sai a buga takara tsakaninsu da matatar ɗangote, kamar yadda ake buga takara tsakanin taliyar ɗangote da ta Bua da kuma ta Golden Penny a kasuwa. 

Masu cin taliya wannan hali da Injiniya Farouk da na Injiniya Kyari suka nuna halaye ne na allawadai, irinsu ne Malama Farida Waziri ta EFCC lokacin Shugaban ƙasa Godluck cewa, tana ganin wasu jagororin ƙasar suna da alamar taɓin hankali har ta ke bayar da shawara a riƙa duba ƙwaƙwalawan ’yan Nijeriya jagorori likaci-lokaci, saboda irin ɓarnar da ta ga su na tafkawa. Mutum ya sa tsinin biro ya saci Naira biliyan 80. Wannan hali ya firgita ta.

Abu ne iri guda, mutum ne ya ɗauki kuɗaɗensa na halal ya zuba a kasuwa, domin miliyoyin jama’a su amfana, amma ka ɗauki ƙwayar ashana ka ƙyasta ka jefa a wannan dukiya da sunan an tare maka hanya. Babu wani ɓoye-ɓoye; kuɗi ne na sata, wanda Malama Farida Waziri take maganarsu.

Wannan fili na Makamashi yana bayar da shawara da a kafa hukuma mai zaman kanta ta likitocin mahaukata da za ta riƙa duba ƙwaƙwalen ma’aikatan gwamnati daga mataki na bakwai har zuwa na 16.

Da zarar an sami wannan ƙwaƙwalwa da alamu cutar hauka komai ƙanƙantarsa a haramta masa yin aiki na amana na gwamnati da na mutane masu zaman kansu. Daga cikin nau’in cututtukan da za a kula da su har da cutar hassada da ƙyashi da rowa da butulci da kuma rashin sanin kishin ƙasa da rashin sanin kishin kai. Babbar cuta da za a duba mutane da ita ce ta rashin sanin yakamata. Duk mutumin da aka same shi da rashin yakamata to, ba shi ba aikin gwamnati har sai ya warke.

Wannan shi ne maganin rashin wuta da rashin man fetur a kasuwar Nijeriya tun da Allah wasu mutane ’yan ƙalilan su hana su.

Duk kuma mutumin da ya yi abin da ya ke da alamar sanin ya kamata to, a girmama shi gwargwadon abin da ya yi. Idan kuma a ka kama mutum da rashin sanin yakamata to, ya tafi lahira!

By ukarofi