Sojojin Nijeriya sun ja kunnen masu zanga-zanga da kakkausar murya a kan ɗaga tutar ƙasar Rasha, wanda su ka ce, yin haka cin amanar ƙasa ne, kuma hukuncin kisa ne.
Janar Chritopher Musa shi ne ya bayyana wannan jan kunnen bayan fitowar su daga wani tattaunawar gaggawa da shugaban ƙasa a yammacin yau Litinin.
Yace” Mun lura da wasu tutoci da ke yawo a cikin ƙasar nan wanda hakan saɓa ma dokar ƙasa ne, don haka muna jan kunnen duk wanda a ka kama da wannan laifin ya ci amanar ƙasa kuma hukuncin kisa ne.
Janar Musa ya cigaba da cewa zanga-zangar an fara yin ta a mastayin ta lumana amma daga baya ta rikiɗe ta koma hargitsi, inda ɓatagari su ka samu damar shiga cikin ta domin yin ɓanna da dukiyoyin gwamnati da na al’ummar ƙasa.
