Mu koyi hana juna ɓarna da yin ba daidai ba

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Mai karatu yau za ka ji rubutuna na wannan makon ya ɗauki wani salo kamar na mai wa’azi to, ba wa’azi ba ne, faɗakarwa ce da tunatarwa daga almajiri mai neman ilimi. Domin shi wa’azi malamai masu tawali’u da tsoron Allah ne ke yin sa, da baki ko a cikin ayyukansu. Na ce haka ne don mu fahimci shi wa’azi ba kawai sai a wajen aikin addini ko a wurin ibada ake yin sa ba. Muna ganin abubuwan wa’azi da dama daga ayyukan malamai da koyarwar su, da kuma abubuwan da ke faruwa a kewayen mu. Idan ka ga wani abu ya faru da ɗan uwanka ko wani maƙwafcinka, shi ma wa’azi ne gareka cewa zai iya samunka.

Addinin Musulunci ya koyar da mu yin taka takatsantsan da rayuwa, da kaucewa fitina ko haddasa rikici, da duk wani abu da zai iya cutar da wani. A cikin ayyukan mu, zantukan mu, da mu’amalar mu ta yau da kullum. Akwai hadisi mai ƙarfi da ke koyar da mu cewa, idan ka ga ana aikata wani abin ƙi wanda bai kamata ba to, ka tsawatar ko ka hana da hannunka ko da bakinka. Idan kuma ka ga maganarka ba za ta yi tasiri ba to, ka nuna fushinka akan abin da ke faruwa, tare da barin wajen. An ce wannan shi ne aiki mafi rauni a cikin rukunan imani.

Haka ma a cikin koyarwar Alƙur’ani Mai Girma, malamai suna tunatar da mu cewa, a duk lokacin da Ubangiji ya ambaci imani to, sai ya goya shi da taimakon juna wajen aikata alheri da yin gaskiya. Wannan yana nuna mana cewa, nasiha ga yin adalci da gaskiya, hana ɓarna da yin ba daidai ba, wani rukuni ne mai muhimmanci a cikin koyarwar addinin Musulunci. Kuma na san ko da a koyarwar sauran addinai ma, aikata alheri da hani ga ɓarna jigo ne mai muhimmanci.

Sai dai a kula da kyau, cewa da ake yi a hana ɓarna ba yana nufin ɗaukar doka a hannu ba ne. Akwai tsari da Ubangiji ya gindaya, haka ma kuma dokokin ƙasa sun tabbatar da shi. Hakkin kowanne ɗan ƙasa ne ya hana ɓarna da karya doka, amma ba ta yadda zai cutar da wani ba, kuma ba tare da ya take haƙƙin kowa ba. Akwai hukumomi da jami’an tsaro, ko wakilan al’umma da alhakin yin hukunci ya rataya a wuyansu. Idan tsawatarwarka da nasiharka ba ta yi amfani ba to, shugabannin al’umma ko jami’an tsaro ne za a kai wa rahoto don su ɗauki mataki.

Shari’a, dokokin ƙasa, da na addini, ba su amince wani ya yi hukunci akan wani ba bisa hurumin doka ba, musamman irin hukuncin da zai iya cutar da mutum ta hanyar taɓa mutuncin sa a matsayin sa na ɗan adam, ko taɓa lafiyarsa ta jiki da ta ƙwaƙwalwa, da kuma uwa-uba ɗaukar ransa, ko yi masa kisan gilla da gangan ko cikin kuskure. Shi ya sa mutum ko ɗan cikinsa ne Shari’a ba ta yarda ya kashe shi ko ya yi masa hukuncin da ya kaucewa doka ba.

Haka kuma, ko da da baki za ka yi wa mutum faɗa ko nasiha, ba a yarda ka yi masa magana cikin ƙasƙanci, ko amfani da kalamai na zubar da mutunci da kimarsa ta ɗan adam ba, kamar zagi da yin amfani da munanan kalamai na wulaƙanci. Ashe kenan za mu fahimci cewa, babban kuskure ne ɗaukar doka a hannu, ko jama’a su yi taron dangi su far wa wani ko wasu don suna zargin sun aikata ba daidai ba, har ma garin haka su hallaka mutum ko su jikkata shi.

Mun ga irin wannan mummunar aika-aika kwanakin da suka gabata a garin Mararrabar Jos da ke Jihar Kaduna, inda wasu ɓatagarin matasa suka yi wa wata malama matar aure kisan gilla, har suka ƙona ta, duk kuwa da ƙoƙarin shiga tsakani don hana su da aka yi. Sakamakon zargin ta da suke yi da shigar burtu don satar yara. An yi makamancin haka a Ƙaramar Hukumar Rano ta Jihar Kano, inda nan ma aka ce wasu matasa sun far wa ofishin ’yan sanda na garin, har suka yi wa wani DPO kisan gilla, saboda zargin yana da hannu a mutuwar wani saurayi da aka kama da zargin sata. Ko a cikin wannan mako mai ƙarewa ma a garin Jos jama’a na cikin alhini na kisan gillar da wasu matasa abokan juna suka yi wa wani matashi da bai jima da kammala karatunsa na jami’a ba, saboda zargin sa da satar waya, zargin da ba a tantance ba.

Wannan ɗanyen aiki ne da rashin hankali da wasun mu ke nunawa akan mutanen da ake zargi da aikata ba daidai ba, kuma ba tare da an tabbatar da laifin su ba. Shi ya sa a baya nake cewa, ɗaukar doka a hannu babban laifi ne, ko da kuwa an tabbatar da zargin da ake yi wa mutum, ballantana kuma babu tabbas, kururuwar shaiɗan ce, da dabbanci.

Lallai akwai buƙatar malamai da sauran masu faɗa a ji su tashi tsaye wajen ilimantar da jama’a illar nuna irin waɗannan halaye marasa kyau, don a kauce musu. Sannan kuma a riƙa hukunta waɗanda aka kama da hannu a aikata wannan ɗanyen aiki, don ya zama darasi ga saura. Ya kamata mu kasance masu girmama ran ɗan adam ko da kuwa ran mai aikata laifi ne, matuƙar hukuma ba ta tabbatar da laifi a kansa ba. Ko da a gaban shari’a ne, ana bai wa wanda ake zargi damar kare kansa, da kuma ’yancin ɗaukar lauyan da zai tsaya masa don tabbatar da ganin an yi masa adalci. 

A koya wa mutane yarda da haƙƙin hukuma wajen binciken mai laifi da gabatar da shi a gaban shari’a. A duk lokacin da aka kama mutum ana zargi, kada a bari wawayen cikin mu su fara kai hannu jikinsa ko far masa da duka. Barin hakan na iya jefa rayuwar sa cikin haɗari, kuma yana nuna cewa babu manya masu tsawatarwa da suka isa su hana aukuwar ɓarna a unguwar, ko yankin da abin ya faru.

A samu wata ƙungiya ko ƙwararru da za su jagoranci horarwa ko gangamin yaƙi da ɗaukar doka a hannu a cikin unguwanni da wuraren ibada, makarantu, tashoshin mota, ta kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta, domin a faɗakar da jama’a, har sai an samar da kyakkyawar fahimta da wayewa kan waɗannan munanan ayyuka.

A yayin da ake kira da a riƙa sa ido kan duk abin da ke faruwa a cikin anguwanni da lungunan da jama’a ke zaune, don hana ɓatagari sakewa su aikata ba daidai ba, hakan kuma ba lasisi ne na ɗaukar doka a hannu ba, a duk lokacin da aka kama wanda ake zargi. 

Allah Ya ba mu zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummar mu. Amin

By ukarofi

Leave a Reply