An kama soja kan roƙar kuɗi a TikTok sanye da kaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An kama wani soja da ke aiki a sashen dakarun sama na Nigerian Army Aviation Hangar a Minnan Jihar Neja, sakamakon bayyanar wani bidiyon TikTok da aka gan sa a ciki yana roƙon wani sanannen ɗan Soshiyal Mediya mai sun King Pedro kuɗi a lokacin da yake sanye da kakin sojoji a jikinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, sojan ya bayyana ne a wani shiri na kai tsaye a kafar TikTok inda ya nemi taimakon kuɗi saboda halin ƙuncin da yake ciki, lamarin da ya sa hukumomin soja ɗaukar matakin kama shi domin gudanar da bincike kan al’amarin, wanda ya bazu a kafafen sada zumunta.

An kama sojan ne a Bataliya ta 234 da ke Badagry a Jihar Legas, duk da cewa yana da alaƙa da wani sansanin soja a Minna, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, Rundunar Sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba kan sakamakon binciken ko matakin ladabtarwa akan jami’in.

Akan haka ne King Pedro da kansa ya yi tir da matakin sojan na roƙar sa kuɗi sanye da kayan sojoji, yana mai hakan cin fuska ne ga kakin soja.

Haka kuam ya gargaɗi sojan da cewa akwai yiwuwar ya fuskanci hukuncin ladabtarwa daga ɓangaren rundunar akan lamarin.

By Babaji

Leave a Reply