Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar dokokin Kano ta dakatar da ciyamomin ƙananan hukumomi 3 na wata uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Ɓagwai na jihar daga aiki na tsawon watanni uku.

Mai taimaka wa gwamnan jihar na Musamman akan harkokin Yaɗa labarai na Zamani, Ibrahim Adam ne ya sanar da haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da ciyamomin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Ɓagwai daga aiki na tsawon watanni uku”, kamar yadda ya rubuta a shafin nasa.

A lokacin aikin haɗa wannan rahoto, babu wani saƙo a hukumance da aka samu akan musabbabin abin da ya sa aka ɗauki wannan mataki akansu ko zargin da ya janyo dakatarwar da aka musu.

By Babaji

Leave a Reply