Shugaban tsaro na ECOWAS ya buƙaci dawo da Mali, Nijar da Burkina Faso cikin ƙungiyar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Juma’a ne shugabannin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS suka yi kira ga dawo da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar cikin ƙungiyar.

A lokacin da ya ke jawabi yayin ziyartar cibiyar kula da lamuran ta’addanci ta Ƙasa, shugaban kwamitin shugabannin tsaro na ECOWAS, Janar Christopher Musa, ya ce dawowar ƙasashen na da muhimmanci wajen tunkarar matsalolin tsaro musamman ɓangaren ƴan tada ƙayar baya.

Ya ce, su na cigaba da ƙoƙari wajen tabbatar da ƙasashen sun dawo, ya na mai jaddada muhimmancin gudunmawarsu ga magance matsalolin tsaro a yammacin Afirka.

Shugaban cibiyar na Ƙasa, Manjo Janar Adamu Laka wanda shi ya karɓi baƙoncin tawagar, ya yi ƙarin haske game da haɗin kan baki ɗaya ƙasashen wajen cin galaba a kan ta’addanci a shiyyar, ya na mai nuna muhimmancin haɗe ƙwarewar duka ɓangarorin tsaron.

By Babaji