
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar ‘Yan sanda ta ce jami’anta sun gudanar da atsayen ne a gidan ƙwadago (Labour House).
Wata sanarwa da hedkwatar Ƴan sandan ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, ACP Olumuyiwa Adejobi ta ce “Ba sakatariyar NLC ba ne aka nufi kai farmakin”.
Rundunar ta ce an shirya atsayen ne kaɗai domin kama wanda ake zargi – wani ɗan ƙasar waje da aka jingina wa laifukan fashi da makami a Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afirka.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta ɗaga murya kan farmaki da jami’an tsaro suka kai sakatariyarta, ta na mai kira da a janye su.
A sanarwar da Adejobi ya fitar ta kafar X a ranar Juma’a, rundunar ta ce a lokacin da ake gudanar da bincike game da kama wanda ake tuhuma da laifukan fashin, jami’a sun kai samame a wani shago da ke yankin Business District a Abuja wanda daga baya aka gano cewa wani sashen gini ne na NLC.
Haka nan, a ranar 7 ga watan Agusta NLC ta fitar da sanarwa cikin wata takarda cewa ta na zargin jami’an ƴan sanda tare da wasu masu baƙaƙen kaya sun farmaki sakatariyarta mai suna Labour House.
Kamar haka, rundunar ‘Yan sandan ta tabbatar da wani rubutu da ke zargin jami’anta sun kai samame Labour House.
