Yadda dandazon masu zanga-zanga ya banƙara shirin ƴan sanda a rana ta 10 a Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da aka kai rana ta ƙarshe a kwanaki 10 na zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, dandazon mutane sun hallara acikin sahun da aka yi wa laƙabi da ‘one-millon-man-march’ a yankunan Apo da Lokogoma da ke Abuja.

Masu zanga-zangar sun sauya wajen gangamin ne daga filin MKO Abiola da Eagles square da aka jibge jami’an tsaro zuwa zuwa Apo da Lokogoma inda su ka taru tun ƙarfe 7 na safe.

A yayin haka ne suka yi ta ɗaga takardun saƙonni tare da rera waƙoƙin “a kawo ƙarshen yunwa” da kuma “dawo da tallafin man fetur”, su na masu kira ga neman canji.

Zanga-zangar wacce aka fara tun ranar 1 ga watan Agusta ta haifar da zaman ɗar-dar inda daga ta lumana sai aka koma sace-sace da salwantar da dukiyar al’umma da ta ƙasa gami da tayar da tarzoma a wasu yankuna.

Hakan ta kai ga ɗaga tutar wata ƙasa da nufin neman agajin gaggawa ko sauya gwamanti wanda hakan ya sa ƴan Nijeriya da dama da suka haɗa da; ɓangarorin tsaro da wasu masu zanga-zangar suka yi watsi da hakan inda a cewarsu yin haka cin amanar ƙasa ne.

By Babaji