Masu zanga-zangar yunwa da matsin rayuwa sun fara taruwa a babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da zanga-zangar mutum miliyan ɗaya.
An hangi masu zanga-zangar ɗauke da kwalaye a rana ta goma na zanga-zangar matsin rayuwan da aka fara run ɗaya ga watan Agusta 2024.
Wakilin Manhaja ya gano cewa, an sami ƙarin jami’an tsaro a tituna na Abuja da filin taro na Eagle Square.
