
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mai Girma Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jinjina wa kamfanin MTN kan bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya da kuma kayan fasahar zamani guda 4,600 domin a raba wa makarantu.
Shettima ya faɗi hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban MTN, Ernest Ndukwe a Fadar shugaban ƙasa.
Ya ce, yunƙurin da MTN ɗin ya yi na tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen magance matsalar tsadar rayuwa abin a yi kwaikwayo ne, domin hakan na nuna ƙoƙarinsa ta fuskar bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya.
Ya kuma ce, ma’aikatar masana’antu da zuba hannun jari tare da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ne za su sarrafa tallafin.
Ya ƙara da cewa, tawagar MTN za ta haɗe kai da ofishinsa wajen tsara waɗanda za su amfana da tallafin kayan fasahar zamanin da raba su a dukkan sassa shida na ƙasar nan.
A lokacin da ya a ke jawabi, shugaban kamfanin ya yaba wa ƙoƙarin gwamnati kan yadda ta tunkaro daidaita taɓarɓarewar tattali a ƙasar ta hanyar shirye-shirye da ma’aikatu, ɓangarori da hukumomi.
