Bankin GT ya yi nasarar daƙile yunƙurin kutse ga adireshinsa na yanar gizo

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Bankin ‘Guarantee Trust’ da aka fi sani da GTBank ya tabbatar da cewa an samu kai hari ta adireshinsa na sadarwa a ranar Laraba.

Sakamakon haka ne jami’an gudanarwa na bankin su ka kasance a ankare inda harin bai yi nasara ba kamar yadda bankin ya tabbatar wa abokan hulɗa da kuma al’umma.

Wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Alhamis, ta ce babu ko ɗaya daga cikin tashoshin sadarwar bankin da aka kutsa wa yayin da ofishin gudanarwarsu ya daƙile harin inda ba a samu buɗewar bayanai na ko da ɗaya ne daga cikin asusun abokan hulɗar bankin ba.

Bankin ya jaddada aniyarsa na cigaba da samar da cikakken tsaro ga dukkan bangarorin kasuwancinsa da ƙoƙarin kare faruwar irin haka a nan gaba.

Haka kuma, ya yi kira ga abokan hulɗa su kasance masu lura tare da gaggauta aiko da rahoton duk wani abin zargi da ka iya zama barazana ga asusunsu da ya bayyana a gare su.

Sauran bayanai za su fito daga baya yayin da bankin ke cigaba da gudanar da bincike game da al’amarin.

By Babaji