An yi kutse a shafin yanar gizon GTBank, wanda yana cikin manyan bankuna a Najeriya.
Lamarin dai ya faru a daren Laraba, wanda ya sa ba a iya shiga shafin kamar yadda wasu kwastomomi suka koka a shafukan sada zumunta.
Duk Ƙoƙarin shiga www.gtbbank.com ya dawo da saƙon kuskure tun daga 10:30 na daren ranar Laraba.
Wani ƙwararre kan harkar tsaro ta intanet da ke da ƙwarewa a harkar bankuna a Nijeriya ya ce mai yiyuwa ne an yi kutse kan bayanan shiga bankin,shi yasa hakan ya faru.
Bankin bai bayar da wani bayani a hukumance ba game da lamarin har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
