
Daga NASIR S. GWANGWAZO
Fadar shugaban ƙasa ta bankaɗo wani yunƙuri na danne kadarorin Najeriya da kamfanin ƙasar China mai suna Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited ya yi a gaɓar tekun Najeriya ta hanyar zamba cikin a aminci.
Kamfanin dai ya so yin amfani da wani hukunci mai cike da ruɗani da wata kotun birnin Paris ta zartas kan jiragen shugaban ƙasar ne da ake kula da su a Faransa inda ya so ƙwace wa Najeriya jiragen nata.
Gwamnatin, ta kuma nisanta kanta da yin duk wata hulɗa da kamfanin na Zhongshan, inda ta ce za ta yi aiki tare da gwamatin jihar Ogùn wacce ke da rikici tsakaninta kamfanin don ganin an wareware taƙaddamar cikin lumana.
Kazalika gwamatin ta sha alwashin fitar da wani tsari da zai ci gaba da fallasa duk wata almundahana a birnin Paris.
Lamarin dai ya samo asali ne tun a shekarar 2007 lokacin da kamfanin Zhongshan ya ƙulla yarjejeniya da jihar Ogun domin gudanar da wasu ayyuka a yankin ciniki a Bagas na freeTrade zone.
Sai dai an soke wannan kwangilar a shekarar 2015, inda aka hau teburin sulhu a shekarar 2016.
Duk da kamfanin bai taɓuka abin kirki a aikin da ya yi alkawarin yi ba, kwamitin shiga tsakanin gwamnatin Ogun da kamfanin ya ci tarar gwamnatin tarayya sama da dala miliyan 60. Abinda gwamnatin tarayyar ta ki amincewa da shi, kuma ta yi nasarar ɗaukaka ƙara a ƙasashen Amurka da Burtaniya inda ita gwamnatin jihar Ogun ta shiga tattaunawa da Zhongshan, wanda a baya-bayan aka kasa cimma matsaya sakamakon dagewar da kamfanin ya yi kan sai an biya shi wannan kuɗi gaba daya.
Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za ta cigaba da kare kadarorin ƙasar daga hare-haren mazambata masu son yin amfani da wasu dokokin rufa-ido wajen cin zalin Najeriya.
