
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ofishin shugaban ƙasa ya yi gamsashshen bayani game da ƙwace jirage uku masu tashin angulu na Nijeriya da wata kotun Faransa ta yi.
A ranar Talata ne kotun ta bayar da umarnin ƙwace jiragen sakamakon wani yarjejeniya da aka ƙulla ba bisa ƙa’ida ba tsakanin gwamnatin jihar Ogun da kuma wani kamfanin ƙasar China.
Kamfanin mai suna ‘Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited’ ya shigar da ƙara kotu ne bayan da gwamnatin Ogun ta dakatar da kwantiragin yarjejeniyar gudanar da harkokin fitarwa tsakanin ta da shi a shekarar 2016..
Saidai ofishin shugaban ƙasa ya ce kamfanin ya yaudari kotun.
Cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta ce Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya na aiki da gwamnatin Ogun don ganin an kawo ƙarshen matsalar.
Onanuga ya yi ƙarin haske kan yadda kamfanin ke ƙoƙarin ƙwace kadarorin gwamnatin Nijeriya da ke waje ta hanyar yaudara.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya ba ta da wani yarjejeniya tsakanin ta da kamfanin Zhongshan, ya na mai cewa damar da kamfanin ke da shi na ƙwace kadarorin ita ce alaƙar da ke tsakanin sa da gwamnatin Ogun.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya tana sane da irin ƙoƙarin da gwamnatin Ogun ke yi wajen ganin an samu hanyoyin shawo kan matsalar.
A shekarar 2007 ne aka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin gwamnatin Ogun da kamfanin Zhongshan wanda a shekarar 2015 ne gwamnatin ta Ogun ta nemi a dakatar da yarjejeniyar sakamakon wasu matsaloli da su ka bijiro wanda hakan ta kai su har cikin shekarar 2016.
Zhongshan ya shigar da ƙara kotun Farisa da ke ƙasar Faransa har sau biyu a watan Maris da Agustan, 2024 inda ya haɗa gwamnatocin tarayya da Ogun a ciki. Kamfanin ya sanya jiragen Nijeriyan uku acikin takardar ƙarar waɗanda an kai su ne domin duba lafiyarsu a ƙasar Faransa.
Saidai, dokar difulomasiyya a faɗin duniya ta haramta wa kotun wata ƙasa shigar da jiragen shugaban ƙasa ƙara kamar dai yadda kamfanin ke ƙoƙarin yi wa na Nijeriya.
