Yadda ‘yan damfara suka yi kutse a WhatsApp ɗin gwamnan Akwa Ibom

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu da ake zargi da damfara sun yi kutse a lambar WhatsApp ɗin Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom, inda suka fallasa wasu bayanan sirrinsa ga abokan hulɗarsa tare da neman wasu abokan hulɗa da su a ba su kuɗi.

Eno, wanda fasto ne da ya kafa All Nations Christian Ministry International, da aka zaɓe shi a bara.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa da yawa daga cikin abokan huldɗar wayar Eno sun samu saƙonni daga lambarsa ta WhatsApp ranar Talata inda ya nemi su tura wani takamaiman adadin kuɗi zuwa wani asusu tare da alƙawarin mayar da kuɗaɗen daga baya wasu kuma sun samu hotunan bayanan sirri.

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ekerete Udoh ya fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa an kulle lambar gwamnan ta WhatsApp da wasu masu laifi da ke yunƙurin damfarar wasu mutane da ba su ji ba gani ba.

Mista Udoh ya ce an sanar da hukumomin tsaro.

“Muna gargaɗin cewa duk wani saƙo da ya bayyana yana neman kuɗi daga waɗannan ‘yan damfara to ya kamata jama’a su yi taka-tsan-tsan kwata-kwata domin ba su fito daga wurin Gwamna ba,” in ji sanarwar.

ƙasa da wata guda da ya wuce, lambobin waya masu alaƙa da wani gwamna sun samu matsala a irin wannan yanayi – Ademola Adeleke na jihar Osun, kawun tauraron Afrobeats Daɓido.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro ta intanet Bilal Abdullahi ya ce kamata ya yi gwamnoni su ƙara tsaro a kan lambobinsu da kuma WhatsApp domin guje wa irin wannan yanayi.

“WhatsApp yana ba da damar ƙarin matakan tsaro ta yadda mutum zai iya haɗa app ɗin zuwa imel ɗinsa don izini kafin amfani da shi sannan kuma akwai abin da muke kira App Lock wanda mutum zai iya kulle aikace-aikacen kuma zai iya amfani da shi kawai idan ya saka pin ko lambar wucewa,” ya shaida wa wannan jarida.

A kwanakin baya ne daraktan hukumar yaƙi da laifuka ta intanet ta Nijeriya (NCCC) Uche Ifeanyi Henry ya shaidawa News Point Nigeria cewa gwamnatin Nijeriya ta kashe biliyoyin nairori kan wata cibiyar yaƙi da laifuffukan yanar gizo ta zamani, domin nuna cewa tana ɗaukar laifukan yanar gizo da muhimmanci.

By ukarofi