Matatar man Ɗangote ta musanta ‘ƙayyade farashin man fetur akan N600 kowace lita’

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar da ke kula da matatar man ɗangote ta yi watsi da rahotannin da wasu ke yaɗawa cewa kamfanin ya ƙayyade farashin man fetur a kan N600 kan kowace lita, inda ta bayyana iƙirarin a matsayin “sanarwa ta hasashe” ba tare da wani tushe ba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na kamfanin ɗangote, Anthony Chiejina ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Wannan musantawa ya biyo bayan rahotannin da wasu jaridu suka yi cewa matatar ta na tattaunawa da ‘yan kasuwar mai, kuma ana iya siyar da mai a kan farashin da ya kai N600 kan kowace lita.

Sai dai kamfanin ya jaddada cewa bai hada kai da ƙungiyar dillalan man fetur ta kƙasa IPMAN ba, kuma za ta riƙa sadarwa ta hanyoyin sadarwa.

Ya ce, “An jawo hankalinmu ga kanun labarai da ke sanar da “Masu Kasuwa N600/lita na ɗangote” da aka buga a Jaridun Punch ranar Talata, 13 ga Agusta, 2024.

“Muna so mu fayyace cewa ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN) ba abokiyar kasuwancinmu ba ce tukuna.”

Ya ci gaba da cewa, “Ba mu taɓa tattaunawa da su kan farashin fetur ba, kuma ba su da wani hurumi ko hurumin yin magana da mu, na alheri ko kuma a ɓoye.

“Muna kira ga jama’a da su nisanta kansu daga irin wannan hasashe. Muna da hanyoyi na hukuma da muke sanar da masu ruwa da tsakinmu ra’ayoyinmu.”

By ukarofi