Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan majalisar tarayya na Dala, Hon. Aliyu Madakin Gini a zaɓen 2013.
Hon. Surajo Imam ya bayyana cewa al’ummar ƙaramar hukumar Dala sun yi dace da sa’a na tura wanda ya jagoranci yi wa yaƙin neman zaɓe wakilci la’akari da kyakkyawan wakilci da yake yi musu.
Ya ce a matsayinsa na wanda ya yi masa Daraktan neman zaɓe yana gode wa Allah da jin daɗin wanda ya tura wakilci Aliyu Sani Matakin Gini yana sauke nauyi a baya sun yi yan majalisun mabambanta aƙalla guda huɗu shi ne na biyar da ba a samu kamarsa ba.
Hon. Surajo Imam ya ce ko kwanan nan ya yi magana akan ƙin yarda da auren jinsi ya ɗaga hannu sau 13 ya yi ƙuduri kuma duk sun wuce harda na ƙin yarda da ƙarin kuɗin wutar lantarki kafin ma matasa su yi zanga-zanga a majalisa ya nuna rashin jin daɗinsa da ɓacin ransa.
Ya ce yanzu Hon Aliyu Madakin Gini ta ɓangaren kawo aiki da raya ƙasa ya kawo tituna guda biyar an kawo a Yalwa da Bulukiya wanda zai haɗa da mazaɓu Takwas an kawo a Gwammaja da Gobirawa inda ya fito ko anan ya yi abinda yakamata.
Hon. Surajo Imam ya ce yanzu ɗan majalisar su yana biya wa yara ɗalibai kuɗin makaranta, zai biya N57M don cigaban ilimin yara, ta kowane ɓangare yana taɓa nan ya taɓa can
Ko da aka baiwa yan majalisar tarayya takin zamani nasu ɗan majalisar ya zo ya rarraba a mazaɓu kwanaki can ma an bashi shinkafa ya kawo ya ba su sun raba wa mutane.
Hon Surajo Imam ya tabbatar da cewa duk abinda shugaban ƙasa Tinubu zai bayar a Dala daga Gwamnatin tarayya kar ya bai wa kowa ya baiwa ɗan majalisarsu Aliyu Madakin Gini ya kawo ya basu domin shi baya riƙe kaya kuma shi a matsayinsa na wanda ya yi wa ɗan majalisar daraktan zaɓe ya gamsu da shi kuma baya da-na+sani a kansa.
