Duk da tarnaƙin magauta bai hana Gwamna Abba aiki ba – Hon Namadi Dala

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kwamishinan bibiyar ayyukan gwamnatin Jihar Kano Hon. Ibrahim Namadi Dala ya bayyana cewa duk da tarin magauta da ke da ƙudurin maida jihar Kano baya, bai hana mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf gudanar da ayyukan ci gaba ba.

Hon. Ibrahim Namadi Dala ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin zantawarsa da su a ofishinsa.

Kwamishinan ya tabbatar da ayyukan alkhairi da gwamnan na Kano yake gudanarwa tare da taimakon muƙarrabansa da ya ba su amana da ya haɗar da shi dake aiki a wannan ma’aikata mai amfani.

Namadi Dala ya ce wannan ya sa ba su yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ci gaba da bibiyar waɗannan ayyuka na mai girma gwamna bayan kama ragamar ayyukansu a matsayin shugaban a wannan hukuma ta bibiyar ayyukan gwamnati.

“A wannan aiki da muke yi muna tabbatar da cewa dukkan ayyukan da ba a ƙarasa ba tun lokacin tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.”

Haka zalika ya ƙara da cewa wannan ayyukan ne da gwamnatin da ta gabata bata kammala ba saboda rashin kishin jihar ya sa a yanzu Injiniya Abba Kabir yake ƙarasawa don amfanin al’umma.

Batun rashin komawar ‘yan kwangila kuwa da aka samu tsaikon komawarsu bakin aiki, Namadi Dala ya ce yana da alaƙa da yadda aka ba su aiki a lokacin baya irin sauƙin kaya sai abinda yake na canjin farashin kayan aiki a halin yanzu.

“Amma kuma yanzu haka dukkan ‘yan kwangilar sun koma bakin aiki bayan zama da mai girma gwamna ya yi da su tare da ba su dukkan abinda ya kamata da haɗin kai don asamu damar ƙarasa wannan ayyuka a faɗin ƙananan hukumomin da muke da su 44.

Sai dai Kwamishinan ya buƙaci al’umma da su ƙara taimakawa wajen addu’o’in da za su kawo zaman lafiya ga wannan jiha kuma su taimakawa gwamnatin nan don samun nasara.

By ukarofi