Uwargidan gwamnan Kebbi ta nemi mata da su shiga noman lambun cikin gida 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris ta yi kira ga mata da su duƙufa wajen noman lambun cikin gidaje.

Ta yi wannan kiran ne yayin da take zagaya gonar lambunta da ke cikin gidan gwamnatin Jihar Kebbi ranar Talatar da ta gabata.

Hajiya Zainab Nasir ta ce ta son noman lambun cikin gida ne bisa ga wani kira da Uwargidan shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinibu ta yi na mata su yi noman lambu a bayan gidajensu a ƙarƙashin wani shirinta mai suna Renewed Hope Initiatiɓe Agricultural Scheme.

Daga cikin kayan lambun da uwargidan Gwamnan take nomawa  sun haɗa da masara, tumatir, alayyahu, dankalin Hausa da na Turawa da dai sauransu.

Ta ƙara da cewa noman lambun nata zai bai wa sauran mata ƙwarin gwiwa wajen fara noman lambu a bayan gidajensu musamman waɗanda ke da wadatar fili a cikin gidajensu.

Ta bayyana cewa yanzu haka uwargidan shugaban ƙasa ta sanya wata gasa da za a iya samun kyautar Naira miliyan ashirin ga matar da noman lambunta ya zamo na ɗaya a cikin wannan shekarar.

Haka kuma ta bayyana cewa a wannan jihar ita ma za ta gudanar da wannan gasar inda za a zaƙulo matan da lambunsu ya fi shahara su wakilci jihar Kebbi a matakin ƙasa.

Daga ƙarshe ta yi kira ga mata da su yi noman lambun gidajensu domin ciyar da iyali da kuma shiga wannan gasar da za a gudanar.

Hajiya Zainab Nasir ta bayyana cewa bayan noman lambu da ta ke yi tana kiwon kifi a ƙoƙarinta na bayar da nata gudunmawar wajen samar da abinci a ƙasa.

By ukarofi