Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce, an baza sojoji zuwa gonaki a sassan arewacin ƙasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
A cewar hedikwatar, an tura sojojin ne domin tabbatar da samun isasshiyar kariya ga manoma daga ’yan bindiga da ’yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a gonakin.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, manoman sun kasance mutanen da ’yan bindiga suka raina, waɗanda ake kai wa hari ba gaira ba dalili da lalata mu su amfanin gona, yin garkuwa da su, har ma da kashe su a wasu lokutan.
Bisa ƙididdigar da wakilinmu ya yi, a rubu’in farko na bana, an kashe manoma sama da 332 a faɗin Nijeriya. Wannan ya nuna an samu ƙaruwar matsalar idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, daga Janairu zuwa Yuni, 2023, inda aƙalla manoma 128 suka rasa rayukansu.
Bugu da ƙari, wani rahoto na baya-bayan nan na cibiyar SBM Intelligence, ya ce, manoma a Arewa sun biya kimanin Naira miliyan 139 a matsayin harajin noma ga ‘yan fashin daji da suka buƙaci aƙalla Naira miliyan 224 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar hauhawar farashin kayan abinci mafi girma da ba a taɓa fuskantar irinsa ba, wanda hukumar ƙididdiga ta Nijeriya ta yi a watan Yuni da kaso 40.87.
’Yan ƙasar sun yi ta kiraye-kirayen a ɗauki matakin gaggawa don magance matsalar yunwa a ƙasar.
Yanzu haka dai ƙungiyoyin manoma a Nijeriya su na yabawa da ɗaukar wannan mataki, wanda ya yi kama da wanda hukumar sibildifens ta ɗauka a Arewa maso Gabas na ƙirƙirar dakarun Agro Rangers, don bayar da kariya ga manoma.
