
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, John Obi Mikel ya bayyana yadda ya ɗauki nauyin biyan kuɗin jirgi ga tawagar Eagles ta ƴan ƙasa da shekaru 23 a lokacin gasar Olympics na shekarar 2016 da aka yi a Rio da ke ƙasar Brazil.
Mikel na ɗaya daga cikin ƴan wasan da shekarunsu ya wuce shiga cikin tawagar kamar yadda mai jagorantar ƙungiyar a lokacin, Samson Siasia ya bayyana.
Mikel wanda tsohon ɗan wasan kungiyar Chelsea ne, ya bayyana yadda gazawar hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, NFF da kwamitin Olympics, NOC ya haifar da koma baya ga burace-buracen ƙungiyar.
Ya ce, “a lokacin da na wakilci ƙasata a Olympics na Brazil, haka mu ka je can. Mu ka jira tun daga safe har dare. Mu na jiran jirgin da zai ɗauke mu ya kai mu Brazil”, kamar yadda ya faɗa a wata hira ta gidan rediyo.
