
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rahotanni sun bayyana cewa an sassari mahaifin ɗan wasan Barcelona Yamal Jamal a wajen wata ma’ajiyar motoci.
Lamarin ya faru da mahaifin Yamal mai shekaru 17, mai suna Mounir Nasraoui a wani yanki na birnin Mataro da ke Arewacin jihar Barcelona a ƙasar Sifaniya.
Wata tawagar mutane da ya yi musayar kalamai da su a ranar Laraba suka hare shi a daren ranar inda suka yi masa aika-aikar.
Ƴan sanda sun tabbatar da kama mutum huɗu da hannu acikin al’amarin a ranakun Laraba da kuma Alhamis.
Baya ga haka ne sai aka garzayawa da shi asibiti cikin mummunan yanayi da ya tsinci kansa yayin da rahotonni ke bayyana cewa ya na samun sauƙi.
