NJC ta amince da Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalai, ta amince da 28 a alƙalan kotuna

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar Alƙalan Nijeriya, NJC ta miƙa sunan Alƙali Kudirat Adetokunbo Motonmori Kekere-Ekun ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wacce suka zaɓa a bai wa shugabar Alƙalan Nijeriya (CJN).

Sannan ta kuma bayar da sunayen wasu 28 ga gwamnoni a don a ba su muƙaman Alƙalan kotuna na jihohi da kuma muƙamin mai Shari’a na kotun Abuja.

An gudanar da haka ne a lokacin zaman Majalisar karo na 106 a ranakun 14 da 15 wanda Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya jagoranta.

Hakan na zuwa na sakamakon wa’adin shugabancin Ariwoola da ya kusa zuwa ƙarshe da kuma lokacin ajiye aikinsa.

A ranar 22 ga watan Agusta ne ake sa ran sakamakon sakon zai fito wanda matuƙar shugaba Tinubu ya amince da Kekere-Ekun a matsayin sabuwar CJN, ta hakan zai nuna ita ce ta biyu cikin mata da suka taɓa riƙe muƙamin bayan Mai Shari’a Mouktar Aloma.

By Babaji