Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Attahiru Jega, rasuwa.
Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega ta rasu ne cikin daren Juma’a sakamakon rashin lafiya a Abuja.
Majiyoyi daga iyalinta sun ce, za a yi jana’izarta bayan idar da sallar Azahar da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana a Babban Masallacin Juma’a na Ƙasa.
Za a binne gawarta ne a maƙabartar Gudu da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hajiya Hauwa ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama, ciki har da fitaccen ɗan jarida kuma marubuci Malam Mahmud Jega da tsohon Babban Darakta na Hukumar Kula da Kadarorin Gwaɓbatin Tarayya, Alhaji Abbas Jega da sauransu.
Marigayiya Hauwa, wacce ta bar ‘ya’yan cikinta 10, ta rasu tana da shekara 86 a duniya.
