Daga ABDULLAHI AHMED a Legas
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Mahauta ta ƙasa, reshan Jihar Legas ta koka da yadda gwamnati ta saka mata haraji mai yawa.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Ahmed ne ya bayyana haka ofishin ƙungiyar jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu ƙusoshin ƙungiyar wanda suka saba yi a duk ƙarshen mako.
Ya ce, shi da sauran mahauta masu gudanar da harkokin sana’arsu ta fawa a Legas suna cigaba da kokawa bisa ga yawan biyan kuɗaɗen harajin dabbobin da suke yankawa a mayankar shanun ta abbatuwa da ke Agege.
Kuma ya shaida wa Jaridar Blueprint Manhaja a Legas gaskiyar wannan al’amari, inda ya cigaba da cewa yana ganin Gwamnatin jihar Legas tana neman ta mayar da su shanun tatsa.
A cewarsa, domin kuwa bayan kuɗaɗen harajin da suke biya a ƙa’idance, a yanzu haka an ƙara ƙirƙiro masu wani harajin wanda idan za ka shiga wurin sayar da dabbobin sai ka biya kuɗin haraji sannan ka shiga.
Ya ƙara da cewa, “hakan ta sanya suka ga ya kamata su zauna su tattauna bisa kan al’amarin, kuma sun zauna sun tattauna har sun yanke hukuncin cewar ba za su cigaba da biyan wannan harajin ba.
“Bisa ga hakan suke son su shawarci Gwamnatin Jihar Legas da ta janye wannan sabon harajin da ta ƙirƙiro musu.
“Da fatan Gwamnatin jihar Legas ɗin za ta ɗauki wannan shawarar tasu bakiɗaya. Haka zalika, ya cigaba da jawo hankulan mambobin ƙungiyar ta mahautan jihar Legas dama ta Nijeriya bakiɗaya da su cigaba da yin haƙuri kuma su bar wa Allah komai dangane da wannan lokacin da al’umma suke ciki na tsadar rayuwa.
Ya cigaba da cewa, “an sani cewa tun daga lokacin da gwamnati ta yi bayanin cewa ta janye tallafin da take yi wa ɓangaren man fetur, ‘yan kasuwa da sauran al’ummar Nijeriya suke ta ƙara shiga ƙuncin rayuwa dangane da wannan al’amari.”
Ya ce, “ya kamata gwamnati ta ƙirƙiro waɗansu hanyoyi waɗanda za su kawo wa al’umma sauƙin wannan ƙuncin rayuwa.
Ya cigaba da bayyana irin cigaban da ƙungiyarsa ta mahautan Abbatuwa ta ke samu a ƙarƙashin jagorancinsa, inda ya ce “kafin samun jagorancinsa ƙungiyar ba ta da gidan sanyi inda ake sanya nama idan ya yi kwantai kuma babu motocin ɗaukar nama kaiwa waɗa su wurare da sauran makamantansu.”
“Amma zuwan su ƙungiyar ta mallaki komai, bugu da ƙari, kuma ga irin tallafin da suke yiwa mambobin ƙungiyar idan sun samu matsala karyewar jari ko rashin lafiya ko kuma kafin zuwa mayankar shanu sanka ya fasama wani maimota gilashin motar ko kuma sanka ya mutu sai su kasa kuɗin kashi uku sai su ba ka kashi biyu ka rage asara da Allah ya ɗora maka,” inji shi.
Ya ce, “da fatan Allah Ubangiji ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya.”
