Afenifere ta buƙaci Tinubu ya bayar da umarnin kafa ‘yan sandan jihohi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Kishin ƙabilar Yarabawa ta Afenifere, ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da ikonsa ya bayar da umarnin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi da ta ƙananan hukumomi.

Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Jare Ajayi, ne ya fitar da sanarwar da ke ɗauke da kiran yau Asabar, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Sanarwar ta ce, ƙungiyar ta yi kiran ne sakamakon rahotannin da ake ta samu na ƙarin hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a a jihohin Ogun da Edo da Ekiti da Oyo da Kogi da Zamfara da kuma Neja, abin da har wata ƙungiya mai bincike ta ayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashe da aka fi satar mutane a duniya.

Ƙungiyar ta ce, ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya tabbatar da kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi da na ƙananan hukumomi ba tare da ɓata wani lokaci ba, ta hanyar bayar da umarni, yayin ake ci gaba da aikin yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima.

Haka kuma ƙungiyar ta Yarabawa ta yi kira da a kakkafa na’urorin ɗaukar hoto na tsaro da sauran kayayyakin fasaha na tabbatar da tsaro a muhimman wurare domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.

By ukarofi