PDP ta zaɓi Abdullahi Tumburkai a matsayin Shugaban ƙungiyar ’Yan Takarar ƙananan Hukumomi a Katsina

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jami’iyar PDP a Jihar Katsina ta zaɓi Honorabul Abdullahi Usman Tumburkai, ƙwararren ɗan jarida daga ƙaramar Hukumar Dandume a matsayin Shugaban ƙungiyar ’Yan Takarar jam’iyyar na zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar.

An gudanar da zaɓen ne a Sakatariyar jam’iyyar da ke Katsina, inda zaɓaɓɓun ’yan takarar jam’iyyar 34 suka hallara a ranar Lahadin da ta gabata.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na sa, Honorabul Hamisu Ismail Jibia.

Sanarwar ta ce, “wannan matsayi yana nuna ƙudirin Abdullahi na samar da haɗin kai na dimokuraɗiyya da kuma samar da hanyar da ’yan takarar jam’iyyar za su yi hulɗa da masu jefa ƙuri’a.

“A matsayinsa na shugaba, Abdullahi Tumburkai zai sa ido kan tsare-tsaren ƙungiyar da nufin inganta gaskiya da samun damar gudanar da sahihin zaɓe.

“ƙungiyar ‘Yan Takarar Jam’iyyar ta zama muhimmiyar hanya ga ‘yan takara don tattaunawa kan al’amuran su, yin cuɗanya da masu zaɓe, da hafa kai kan batutuwan da suka fi ci gaban al’umma.

Abdullahi Tumɓurkai nuna matuƙar farin cikin sa da zaɓar sa a matsayin shugaban ƙungiyar ‘yan takarar PDP. Ya ce, wannan rawar wata dama ce ta haɗa muryoyi daban-daban da kuma tabbatar da cewa duk ‘yan takara sun samu damar raba ra’ayoyinsu game da makomar ci gaban al’ummar.

Ya ce, “Na himmatu wajen samar da yanayi mai kyau, inda masu jefa ƙuri’a za su iya yanke shawara na gaskiya.”

Honorabul Abdullahi Tumburkai ya ƙwararre ne a harkokin siyasa wanda hakan ya sa ya dace ya jagoranci ƙungiyar.

ƙwarewarsa a wannan fanni zai taimaka wajen jagorantar ‘yan takara ta hanyar kai su ga cin nasara a zaɓe.

By ukarofi