OCSC ta buƙaci Tinubu ya mayar da tallafi man fetur

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na fuskantar matsin lamba na maido da tallafin wutar lantarki da man fetur, yayin da ƙungiyoyin farar hula a jihar Osun suka yi gargaɗin yiwuwar sake ɓarkewa da zanga-zanga matuƙar ba a biya musu buƙatunsu ba.

Gamayyar ƙungiyoyin farar hula na jihar Osun (OCSC) da ke wakiltar aungiyoyin fararen hula daban-daban a jihar, sun fitar da sanarwa a ƙarshen zanga-zangar ta #EndBadGovernance na kwanaki 10, inda ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban OCSC Waheed Lawal, ta soki jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a faɗin ƙasar kwanan nan game da zanga-zangar.

ƙungiyar ta bayyana rashin gamsuwarta da matakin da gwamnati ta ɗauka, sannan ta yi gargaɗin cewa nan ba da jimawa ba matasan Nijeriya za su koma kan tituna domin neman ingantacciyar shugabanci.

Lawal ya jaddada buƙatar gwamnati ta aiwatar da tsare-tsare da za su magance matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, maimakon dogaro da raba kayan tallafi ga jihohi.

Ya kuma yi kira da a saki dukkan masu zanga-zangar da aka tsare.

“An kawo ƙarshen zanga-zangar #EndBadGovernance a hukumance a yau, amma abin takaici ne yadda shugaban ƙasa bai yi magana kan muhimman batutuwan da masu zanga-zangar suka gabatar ba. 

Shugaba Tinubu ya yi magana, amma ya yi buris da kukan ‘yan Nijeriya da ke fama da yunwa a kullum,” inji Lawal.

“Muna buƙatar a maido da tallafin man fetur da wutar lantarki, saboda cire su ya haifar da babbar illa ga ‘yan ƙasa, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.

ƙungiyar ta kuma buƙaci a gaggauta sakin duk masu zanga-zangar da a halin yanzu ke hannun ‘yan sanda, ciki har da waɗanda ake tsare da su a lokacin zanga-zangar #EndSARS, tare da yin kira da a biya su diyya kan take haƙƙinsu na ɗan Adam.

“OCSC ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar ɗaukar matakin hana tashe-tashen hankula. Idan har Shugaban ƙasa ya ci gaba da yin watsi da buƙatun ‘yan Nijeriya, za mu shirya wani gagarumin gangami na ‘yan ƙasa da matasa masu ɗa’a, domin gudanar da wani zagaye na zanga-zangar da nufin samar da ingantacciyar Nijeriya,” inji sanarwar. 

By ukarofi