Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta wato Bauchi State Independent Electoral Commission (BASIEC), ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓuka a ƙananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi, yadda za a zaɓi shugabanni da mataimakan su da kansiloli 323, a ranar 17 ga watan Augusta 2024.
Shugaban hukumar ta BASIEC Alhaji Ahmed Makama shi ne ya bayyana haka a taron ‘yan jarida da ya kira a ofishinsa.
Alhaji Ahmed Makama ya bayyana cewa sun yi zama da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan zaɓe lokuta da dama sun bayar da haɗin kai, komai ya kankama don gudanar da zaɓen.
Don haka Hukumar Zaɓen ta BASIEC tuni ta sayar da takardun cikewa na shugaban ƙaramar hukuma da mataimakin sa kan naira dubu 200 da kuɗin aiki naira dubu 50. Ta sayar da takardar cikewa domin shiga zaɓen kansiloli kan naira dubu 100 da kuɗin aiki naira dubu 20.
Za a gudanar da zaɓen a dukkan mazaɓun ƙananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi kamar yadda ake gudanar da sauran zaɓukan ƙasa.
Don haka Shugaban hukumar ta BASIEC Alhaji Ahmed Makama, ya bayyana godiya ga shugabannin dukkan hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya da ke Bauchi saboda halartar dukkan zaman da Hukumar Zaɓen ta yi da su. Ya gode musu saboda ba su goyon baya na zuwa da kan su ba tare da tura wakilci ba.
Haka jam’iyyun siyasa ya yaba musu game da yadda suka halarci dukkan zaman da hukumar ta kira su, aƙalla jam’iyyun 18 sun turo shugabanni da wakilai an zauna da su tare da sauran masu ruwa da tsaki, kuma kowa ya bayar da gudummowar da ta dace a yayin zaman.
Don haka Shugaba Ahmed Makama, ya buƙaci matasa su shiga harkokin zaɓen ƙananan hukumomi da zai gudana don a dama da su saboda su amfana.
Ya ƙara da cewa rashin taka muhimmiyar rawa da wasu mutanen ƙwarai masu aƙida ke yi, shi ke haifar da kowane mutum ya fito ya tsaya idan ya samu nasara kuma ya jagoranci mutane ta hanyar da ba ta dace ba.
Shugaban hukumar zaɓen Alhaji Ahmed Makama ya bayyana cewa kuskure ne mutum ya ɗauki siyasa a matsayin aikin marasa alƙibla ko aikin yi, don haka ya ce mutane su lura da yadda ake takara a tafi wakilci a gama a dawo gida kuma a samu alheri ga wanda aka wakilta.
Kuma wanda ya wakilci yankin ku haka za a ba su dukiyar ku su sarrafa ta yadda suke so. Amma idan mutane masu alkibla suka shiga dole su nemi shawara game da irin ayyukan da kowane yankin ya ke bukata a kuma yi musu abin da zai amfane su.
Game da ƙorafi da wasu jam’iyyun adawa ke yi na ganin ba za a musu adalci ba lokacin zaɓen, ya bayyana, shi zaɓe abu ne mai sauƙi duk wanda ya shiga takara ya nemi goyon bayan mutane idan suka zaɓe shi tun a rumfunan zaɓe za a ƙirga a bayyana wanda ya samu nasara a kuma sanar ba wanda zai tauye dan takara.
Don haka ya buƙaci kowa ya kwantar da hankalin sa ya nemi goyon bayan masu zaɓe wannan hukumar za ta yi dukkan adalci wajen bayyana wanda suka samu nasara.
Don haka ya ce za a gudanar da zaɓukan da katin zaɓe na gwamnatin tarayya ne kuma hukumar zaɓe ta ƙasa da hukumomin tsaro za su sa ido don ganin an yi zaɓe na gaskiya duk jamiyyar da ta samu nasara za a bayyana sunan ɗan takararta don haka mutane su daina kokonto, su nemi goyon bayan masu zaɓe su shiga a dama da su don bayar da tasu gudummuwar.
