
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kwamitin zaman lafiya na ƙasa, NPC ya bankaɗo wata maƙarƙashiya da aka samu daga ƴan jam’iyyu a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ganin yadda aka matsa masa kan sai dai ya tunzura hukumar zaɓen ta ƙasa (INEC) ta datakar ko kuma soke zaɓen.
Kwamitin, wanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar AbdulSalami Abubakar ke jagoranta, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a Abuja, a lokacin da ya gabatar da rahotonsa mai ɗauke da shafuka 106 na zaɓen 2023 mai suna; “Nigeria’s Pursuit of Electoral Compliance: National Peace Committee NPC 2023 General Elections Report”.
Da farko, kwamitin ya gana da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da sauran jami’an hukumar gudanarwa na hukumar inda ya gabatar mu su da jawabi kan shirye-shiryen zaɓen jihohin Edo da Ondo da ke tafe.
Rahoton ya ce, kwamitin ya samu kiraye-kiraye da ƙararraki dama kan ya sanya baki game da dakatar da sanar da sakamakon zaɓen.
Hakan na zuwa ne sakamakon karya wasu dokokin zaɓe a yayin karɓa da shigar da sakamakon aka ce an yi don haka a dakatar da karɓa tare da soke zaɓen.
Wasu masu sharhi kuwa, cewa suka yi, NPC ta nemi a soke zaɓen saboda wanda ya yi nasara bai samu kaso 25 da ake nema ba kamar yadda dokar zaɓen ta nuna.
Saidai, rahoton ya ce wannan mataki ne da hukumomin da ke da alhakin yin hakan ya kamata a nemi su akan batun ba NPC ba, ya na mai cewa ba huruminsa ba ne.
