
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wasu mutane shida a ƙauyen Karikari da ke ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano sun rasa rayukansu sakamakon cin ɗan wake.
Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis a gidan wani marigayi mai suna Malam Abdulkarim.
Wani maƙofcin gidan, Garba Muhammad ya bayyana wa manema labarai cewa saboda tsananin rayuwa da yunwa, matar wacce ke ƙoƙarin ciyar da iyalanta ta yi amfani da gurɓataccen garin alabo wajen yi mu su girki.
Ya ce, “cin abincin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida cikin ahalin, har da mahaifiyar.”
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mutane shida da suka ci abinci an garzaya da su babban asibitin Gwarzo inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.
Ya ce, an fara gudanar da bincike domin tabbatar da haƙiƙanin abin da ya sabbaba mutuwarsu.
