Ƴan bindiga sun kashe na hannun daman gwamnan Katsina da matarsa a ƙauyensu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta tabbatar da rahoton kisan Sanunsi Gyaza, wani na hannun daman gwamna Dikko Raɗɗa na jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Sadiq ya bayyana wa manema labarai ta wayar tarho a ranar Lahadi inda ya ce su na sane da al’amarin kuma suna gudanar da bincike a kai.

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a da dare inda rahotanni suka bayyana cewa, ƴan bindigar sun kashe Sanusi ne a gidansa da ke Gyaza a ƙaramar hukumar Kankia wanda a sanadiyyar haka, matarsa ta farko ita ma ta rasa ranta.

Haka kuma, ƴan bindigar sun yi garkuwa da matarsa ta biyu a yayin harin.

Gyaza shi ne tsohon shugaban ƙungiyar malamai ta ƙaramar hukumar Kankia.

Kazalika, faruwar al’amarin ya ƙara nuna yadda kashe-kashe da ayyukan garkuwa da mutane ke cigaba da ta’azzara a jihar.

A lokacin tattara rahoton, an nemi Darakta-Janar na yaɗa labarai na gwamnan, Mai-Wada Ɗan-Malam, amma ba a same shi ba kuma bai amsa saƙon da aka ma wayarsa ba.

By Babaji