Wani magidanci ya buƙaci kotu ta raba aurensa da matarsa bisa zarginta da cin amanar aure da yin hira da makwabcinsa ta shafukan sada zumunta.
Da ya ke jawabi a gaban kotun, magidancin ya zargi matarsa cewa sau uku tana tafiya ta bar gidansa, ciki har da wani lokaci da ta bar gidan nasa na tsawon wata biyu.
Ya kuma zarge ta da alaƙa da wani makwabcinsa wanda ta ke ɗaukar tsawon lokaci tana hira da shi ta intanet.
Ya ce, “lokacin ƙarshe da ta bar gidan sai da ta daɗe kafin ta dawo, da ta dawo kuma sai ta kwashe kayanta.
“Na gaji da yadda ta ke wulaƙanta zaman aure, saboda haka ina buƙatar kwanciyar hankali,” inji shi.
Amma a martaninsta, matar ta bayyana wa kotun cewa mijin nata, “ba shi da haƙuri, yana zargi na da cin amanar aure ba bisa haƙƙi ba, har ya taɓa sawa an tsare ni a sel ɗin ’yan sanda.
“Na yarda a raba auren, na gaji da yadda ya ke duka na, zargin cin amanar auren ya ishe ni haka.”
Daga ƙarshe kotun da ke zamanta a Ighando a Jihar Legas ta raba auren saboda abin da ta kai ga cin amana, sakaci da aure da kuma rashin zama tare.
Shugaban kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce, raba auren shi ne zai kawo ƙarshen taƙaddamar, sannan ya umarci mijin da ya biya matar Naira dubu 250.
