Yadda kurma ta lashe gasar sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu

Spread the love

Mia le Rouɗ, ta zamo kurma sarauniyar kyau ta farko da ta lashe gasar kyau da aka yi a Afirka ta Kudu bayan takaddamar da aka samu a batun zaɓen wadda tafi kyau, inda ɗaya daga cikin masu fafatawar a gasar ta janye saboda zarginta da kasacewa ’yar Nijeriya.

A jawabinta na godiya bayan sanar da wadda ta yi nasara,Ms Le Rouɗ, ta ce tana fatan nasararta za ta ƙarfafa gwiwar waɗanda ke ganin ana ware su a cikin al’umma.

Ta ce tana so ta taimakawa waɗanda ba su da arfi da kuma waɗanda ke ganin ba su da damar iya shiga gasar.

A makon da ya gabata Chidimma Adetshina, mai shekara 23, ta fita daga gasar bayan zarge-zargen da aka yi mata cewa mahaifiyarta ba ‘yar Afirka ta kudu ba ce.

Ms Adetshina, an haife ta a Afirka ta Kudu, amma mahaifinta ɗan Nijeriya ne yayin da mahaifiyarta kuma ‘yar asalin Mozambiƙue ce.

An riƙa caccakarta a shafukan sada zumunta ciki har da wani minista inda ake cewa ba ta da damar wakiltar ƙasar saboda kasancewarta ba ‘yar ƙasa ba.

Ms Le Rouɗ, mai shekara 28, ta gamu da lalurar rashin ji ne tun tana da shekara ɗaya a duniya, inda aka sanya mata na’urar taimakawa wajen jin magana.

Ta ce, sai da ta shafe shekara biyu ana koya mata magana kafin ta iya furta kalmominta na farko a duniya.

By ukarofi