Birtaniya za ta wahala idan likitocin Nijeriya suka bar ƙasar – Farfesa Pate

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan lafiya na Nijeriya Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce ma’aikatar lafiya ta Birtaniya, (NHS) za ta yi fama idan ma’aikatan lafiya ‘yan asalin Nijeriya suka bar aiki a ƙasar.

Pate ya ce a duk duniya ana neman ma’aikatan lafiya na Nijeriya, kuma kashi 67 cikin ɗari na ma’aikatan suna aiki ne a Birtaniya.

Kuma kashi 25 cikin ɗari na ma’aikatan lafiya na gwamnatin Birtaniya, ‘yan Nijeriya ne.

Ministan ya ƙara da cewa ana son likitoci Nijeriya da ma’aikatan jinya kuma wannan abu ne da ƙasar za ta yi alfahari da shi.

Ministan ya bayyana hakan ne a hirar da tashar talabijin ta Channel ta yi da shi a yau Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma yi magana a kan sabuwar manufar Nijeriya a kan ficewar ma’aikatan lafiya na ƙasar, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ita, da za ta yi maganin barin ƙasar da ma’aikatan lafiyar ke yi zuwa ƙasashen waje.

By ukarofi