Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya za ta ɗauki malamai 3,500 da za su koyar a makarantun gaba da firamare na haɗaka na tarayya 3,500 a faɗin ƙasar.
ƙaramain ministan ilimi Dr Yusuf Sununu, ne ya sanar da haka a wajen wani taron kwana biyu na masu ruwa da tsaki a kan makarantun sakandire a Nijeriya.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar, (NAN), ya ruwaito cewa an shirya taron ne domin tattauna matsalolin da damun harkar ilimin sakandire a Nijeriyar.
Ministan wanda ya ce ɗaukar malaman za ta bunƙasa ilimi, ya tabbatar cewa, ma’aikatar na haɗa hannu da ofishin shugabar ma’aikata ta tarayya da hukumar ma’aikatan tarayya da sauran hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin ɗaukar malaman 3,500.
Ya kuma ƙara da cewa an samu amincewar gina ƙarin makarantu na musamman 50 a faɗin ƙasar domin bunƙasa koyo da koyarwa.
