
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da damina ke cigaba da ƙamari, hukumar bada agaji ta gaggawa ta jihar Kaduna, KADSEMA ta gargaɗi mutanen da ke zama a yankunan da ke tattare da barazanar ambaliya su ƙaurace zuwa wasu wuraren domin guje wa faɗawa cikin haɗari.
Cikin Wata sanarwa da sakataren hukumar, Usman Mazadu ya fitar, ya ce aƙalla ƙananan hukumomi bakwai ne ke cikin haɗarin riskar ambaliya musamman yankunan da ke kusa rafuka da kuma yawaitar mamakon ruwan.
Hukumar ta ce ya zama wajibi ta sanar da al’umma musamman la’akari da ruwan sama da aka yi ta yi a ranakun 18 da 19 ga watan Agusta wanda har yanzu ana cigaba da yi.
Sanarwar ta ce, yankunan ƙananan hukumomin sune kamar haka; Government Secondary School Kigo Road, LEA Primary School Unguwar Rimi da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, Namadi Sambo Skill Acquisition Center Tudun-Wada da kuma LEA Primary School Nasarawa a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.
Sauran sune; Government Secondary School Narayi a ƙaramar hukumar Chikun da masallacin Juma’a Hayin Malam Bello a ƙaramar hukumar Igabi.
Sai kuma yankunan wasu ƙananan hukumomin da su ka haɗa da; makarantun LEA na Agwom da Tsauni a Sanga; da makarantun LEA na Jere a Kagarko; da kuma GSS Kafanchan a Jama’a.
