
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta sanar da gwamnatin tarayya batun shirinta na shiga yajin aiki nan da mako uku masu zuwa.
Rahotanni sun tabbatar da hakan daga Majalisar ASUU ta Ƙasa a wani zama da ta yi a jami’ar Ibadan ta jihar Oyo yayin da za a aika da saƙon hukuncin nata zuwa ga ma’aikatun ƙwadago da na ilimi.
Ƙungiyar ta ce ta yi haka ne don tabbatar da cewa matakan da su ke ɗauka sun yi daidai da yadda doka ta tsara.
A kwanakin baya ne ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki kasancewar ba a zartar da yarjejeniyar da aka ƙulla ba tsakanin ta da gwamnatin tarayya.
Sannan a ranar 26 ga watan Yuni ne Ministan ilimi, Tahir Mamman ya gayyaci ƙungiyar wani zama don tattauna batun janye tafiya yajin aiki inda shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce sakamakon zaman shi ne har yanzu gwamnati ba ta zartar da alƙawuran da yi mu su ba.
