Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya tsige Arabi tare da maye gurbinsa da Usman a matsayin shugaban NAHCON

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar jigilar alhazan Nijeriya, NAHCON.

Farfesa Usman sanannen malamin addini ne daga cibiyoyin ilimi na Jami’o’in Madina da Peshawar a ƙasar Pakistan.

Ya kuma goge a ɓangaren harkar jigilar alhazai sakamakon taɓa riƙe muƙamin shugaban hukumar reshen jihar Kano wanda kuma a yanzu ya zama na ƙasa baki ɗaya.

Naɗa farfesan da Tinubu ya yi zai biyo bayan tabbatar da shi ne daga Majalisar Dattijai.

Kazalika, Tinubu ya ce ya na kyautata zaton cewa sabon shugaban hukumar zai gudanar da aikinsa cikin tsari tare da tabbatar da gaskiya da kuma ƙoƙarin biyayya wa ƙasa.

By Babaji